Mutane 69 gobarar daji ta kashe a Aljeriya

Mutane 69 gobarar daji ta kashe a Aljeriya

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon gobarar daji a Aljeriya ya karu zuwa 69.

A yayin taron manema labarai da Babban Mai Gabatar da Kara na jihar Tizi Vizu da ke da nisan kilomita 100 gabas da Babban Birnin Kasar Abdulkadir Umayrush ya gudanar, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu mutane 69 da suka hada da sojoji 28 da fararen hula 41 ne suka mutu sakamakon gobarar dajin.

Umayrush ya kara da cewa, akwai yiwuwar daruruwan mutane sun rasa rayukansu amma ya zuwa yanzu ba a gama gano hakan ba, ya yi ikirarin cewar wasu makiya kasar ne suka cinna wutar.

A gefe guda, Aljeriya ta sanar da zaman makoki na kwanaki 3 sakamakon gobarar dajin.

Fadar Firaministan Aljeriya ta bayyana cewa, sun kulla yarjejeniya da Tarayyar Turai don dakko hayar jiragen sama masu kashe gobarar daji.

Sanarwar ta ce, jiragen da aka haya su ne aka yi aikin kashe wutar daji da ta kama a Girka kuma daga ranar Alhamis din nan za su fara aiki a Aljeriya.

Gobarar daji ta bulla a yankuna 71 da ke jihohi 18 na Aljeriya.


News Source:   ()