Mutane 620 ne ke mutuwa duk rana sanadiyar haɗarin mota a nahiyar Afirka

Mutane 620 ne ke mutuwa duk rana sanadiyar haɗarin mota a nahiyar Afirka

Duk da yadda nahiyar ta Afrika ba ta da cunkoson ababen hawa sosai, hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce a nahiyar, haɗurran motoci ne suka fi laƙume rayuka.

Saɓanin sauran yankunan duniya da matsaloli masu alaƙa da gudun wuce ƙima, ko tuƙi cikin maye ko kuma rashin sanya ɗamarar tuƙi, ko hular kariya ke zama silar haɗurran ko kuma asarar rayuka a kan tituna, WHO ta ce rashin kyawun hanyoyi shi ke a matsayin dalilan hadurran motar tare da sabbaba asarar rayuka.

A cewar alƙaluman ƙwararrun na Majalisar Ɗinkin Duniya, baya ga rashin kyawun hanyoyin, matsaloli masu alaƙa da rashin wadatattun kayakin kai ɗaukin gaggawa, ciki har da motocin ɗaukar marasa lafiya na matsayin dalilan da ke ta’azzara asarar rayuka sanadiyyar haɗurran motar.

Ƙarancin kayakin more rayuwa, lalacewa, ko kuma tsufan motocin da ke sintiri a kan tituna, rashin wadattun matakan kariya na daga cikin ƙarin dalilan da ke haddasa yawaitar haɗarin mota a nahiyar ta Afrika.

WHO ta ce yanzu nahiyar ta Afrika ta zarta hatta yankin kudu maso gabashin Asiya a yawan a haɗurran mota, inda alƙaluma ke nuna cewa mutane 19 na mutuwa a duk mutum dubu 100 sanadiyyar haɗarin mota a Afrika.

Nahiyar Afrika ita ke da ɗauke da kashi 19 cikin 100 na adadin mutanen da haɗarin mota ya hallaka a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)