Mutane 61 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu sakamakon kifewar wani jirgin ruwa dauke da 'yan gudun hijira a gabar tekun Tunisiya.
Daraktan Shiyya na Hukumar Kare Fararen Hula ta Tunisiya Murad Al-Mishri ya bayyana cewar an sami gawarwakin 'yan gudun hijira 61 wadanda suka taso a jirgin ruwa daga Tsibirin Kerkennah na yankin Safaks a ranar 6 ga Yuni, wanda daga baya jirgin nasu ya kife.
Mishri ya kara da cewar 28 daga cikin gawarwakin da aka ciro daga teku mata ne, maza manya 30 da yara kanana 3.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da binciken ciro sauran 'yan gudun hijirar da suka bata.