Mutane 60 ne suka mutu sakamakon kifewar wani jirgin ruwa a kogin Mai-Ndombe da ke yammacin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Ministan Taimakon Jin Kai Steve Mbikayi ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter inda ya bayyana cewa, jirgin ruwan da ke dauke da mutane sama da 700 ya kife.
Mbikayi ya shaida cewa, za a gurfanar da wadanda suke da hannu a hatsarin a gaban kotu, an ciro jikkunan mutane 60 inda aka kubutar da wasu 300.
Ana ci gaba da aiyukan ceton jama'a.
Ana yawan samun hatsarin jiragen ruwa a kasar saboda yadda ake daukar mutane da kaya da suka wuce kima.