Mutane 42 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar zazzabin Lassa da ake dauka daga bera da dangoginsa.
Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta shaida cewa, karin mutane 6 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar da ake dauka daga beraye.
Rasuwar mutanen 6 ya kawo adadin wadanda suka mutu daga watan Janairu zuwa yau ya tashi zuwa mutum 42.
A wannan lokaci kuma, cutar ta kama mutane 191 a jihohin Edo, Ondo, Kaduna, Taraba, Ebonyi, Plateau da Bauchi.
A shekarar 1969 ne cutar zazzabin Lassa ta fara bulla a Najeriya, kuma baya ga kasar, an samu bullar ta a kasashen Mali, Togo, Gana, Laberiya da Saliyo.
A shekarar 2019, gwamnatin Najeriya ta aiyana dokar ta baci game da cutar Lassa a kasar.
A kowacce shekara a lokacin da ake samun daukewar ruwan sama a tsakanin watannin Nuwamba da Mayu, kamuwa da cutar ta zazzabin Lassa na karuwa sosai a Najeriya. A Shekarar 2019 mutane 129, a 2020 kuma sama da 300 ne cutar ta yi ajali a kasar.
Ana daukar cutar mai kisa daga kashin bera, kuma mai dauke da ita na iya harbawa wani.
Mahukunta na yawan gargadar jama'a kan su bayar da muhimmanci wajen tsafta, sannan su guji kusantar bera da sauran dabbobi makamantansa.