Adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon fashewar tankar mai a jihar Kogi da ke arewacin Najeriya, an kuma aiyana zaman makoki na kwanaki 2.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kogi Kingsley Fanwo ya shaida cewar, fashewar ta afku a yankin Felele na jihar da ke kan har Lokoja-Abuja, kuma adadinw adanda suka mutu ya kai mutane 15, wasu 15 sun jikkata.
Fanyo ya ce sakamakon wannan ibtila'i an aiyana ranakun 25 da 26 ga Satumba a matsayin ranakun zaman makoki a jihar.
A gefe guda, Fadar Shugaban Najeriya ta rawaito Shugaba Muhammadu Buhari na fadin ya ji takaicin afkuwar hatsarin.
Sanarwar ta ce, Shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyya da jaje ga iyalai da makusantan wadanda suka mutu, ya kuma yi fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka.
A ranar Alhamis din nan ne wata tankar mai ta ci karo da kananan motoci 5 a hanyar Lokoja-Abuja inda nan take gıbara ta tashi.