Adadin mutanen da cutar kwalara ta yi ajalii a Najeriya ya karu zuwa 296.
Mukaddashin Sakataren Hukumar Lafiya da Hidimtawa Jama'a Dakta Muhammad Kawu ya bayyana cewa, a Abuja an sake gano mutane 91 dauke da cutar Kwalara, kuma wasu mutane 7 sun mutu.
Hakan ya kawo adadin wadanda cutar ta kashe a fadin Najeriya zuwa 296.
Kawu ya kara da cewa, an aike da magunguna zuwa ga yankunan da aka samu bullar cutar.
Tun daga watan Janairu zuwa yau kusan mutane dubu 11 cutar kwalara ta kama a Najeriya.
Sakamakon matsalolin rashin tsaftataccen ruwan sha da magani a kan kare ya sanya cutar kwalara na kashe mutane da dama a Najeriya.