Adadin wadanda suka mutu sakamakon rushewar wani gini mai hawa 10 a Alkahira Babban Birnin Masar ya kai mutane 23.
Jami'an tsaron farar hula sun bayyana cewa, sun sake gano jikkunan mutane 5 a karkashin ginin mai hawa 10 da ya rushe a yankin Gadar Suwaish da ke gabashin Alkahira.
Jaridar gwamnatin Masar ta Al-Ahram ta sanar da cewa, mutane 23 ne suka mutu, wasu 25 kuma suka samu raunuka sakamakon rushewar ginin.
Da fari an ciro jikkunan mutane 18 daga karkashin buraguzan ginin.
Har yanzu babu wata sanarwa da gwamnati ta fitar game da musabbabin rushewar ginin, amma wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta ce, gini ya rushe sakamakon kwaskwarima da aka yi masa.