Rahotanni daga kasar na bayyana cewa tun a watan Satumba ne aka soma fuskantar mutuwar mutane bayan da suka ci abinci mai dauke da guba.
Kasar ta sake samun wani wanda abin ya shafa wanda a ranar Laraba, aka sanar da mutuwar wani yaro dan shekara biyar a Soweto. Gwamnati ta ayana wannan iftila’I a matsayin "bala'i na kasa" da kuma daukar matakan da suka dace don shawo kan wannan matsala.
Wasu daga cikin shagunan da ake sayar da wadanan abinci masu guba a Afrika ta kudu © EMMANUEL CROSET / AFPWasu rahotanni na bayyana cewa akasarin abincin da mutane ke ci,na daga cikin abincin da ya gurbace, wanda galibi ana amfani da shi wajen noma, amma ana sayar da shi ba bisa ka'ida ba, kuma 'yan Afirka ta Kudu da yawa ke amfani da su wajen yakar beraye. An gudanar da gwaje-gwaje a gundumar Naledi, inda yara shida suka mutu a watan Oktoba, kuma an gano alamun wadannan magungunan kashe kwari a cikin shagunan.
Wasu daga cikin kananan shaguna na cikin gida da ake kira Spaza,shagunan na cikin garuruwa,hukumomin sun bayyana cewa, matsalar ba ta tsaya ga wadannan shagunan spaza kadai ba, kuma wadannan sinadarai suna nan a wurare da dama kama daga kasuwani.
Ya kamata a karfafa sa ido kan shagunan da ke sayar da abinci, kuma nan ba da jimawa ba masana kimiyya da yawa za su shiga cikin tawagar ministocin, domin tsara matakan rigakafin na dogon lokaci. Yayin da ake ci gaba da fusata a yankunan da yara suka mutu, tare da nuna kyamar baki a shagunan da ‘yan kasashen ketare ke yi, gwamnati ta gargadi jama’a kan yunkurin daukar doka a hannunsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI