Jimillar mutane 137 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da aka kai a wasu kauyuka da ke Nijar a iyakar kasar da Mali.
Kakakin gwamnatin Nijar Zakaria Abdourahmane ya yi bayani a tashar talabijin ta kasa cewa, an kashe mutane 137 sakamakon hare-haren ta'addanci da aka kai a ranar Lahadi a kauyukan Bakorat da Wistane da ke yankin Tahoua.
Da farko an sanar da mutuwar mutane 30 kawai.
A makon da ya gabata ma 'yan ta'adda sun kai hari kan 'yan kasuwa da ke dawowa daga cin kasuwa a yankin Tillaberi na Nijar inda suka kashe mutane 58. Hakan ya sanya an aiyana zaman makoki na kwanaki 3 a kasar.
A watan Janairu ma an kai hare-hare a kauyukan Tchombangou da Zaroumdareye inda aka kashe akalla mutane 100.
A 'yan shekarun nan kasashen yankin Sahel 3; wato Burkina Faso, Nijar da Mali na fuskantar hare-haren 'yan ta'addar Daesh da Alka'eda.