Mutanen da ambaliyar ruwa ta yi ajali a kasar Sudan sun kai mutum 124.
Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Sudan ta bayyana cewar, tsawon wasu 'yan watanni ake ta samun mamakon ruwan sama a kasar wanda ya janyo ambaliyar ruwa. Ya zuwa yanzu mutane 124 ambaliyar ruwan ta kashe.
Gidaje sama da dubu 100 sun rushe ko sun lalace sakamakon ambaliyar ruwan.
A ranar 3 ga Satumba Majalisar Tsaro ta Kasa ta Sudan ta aiyana dokar ta baci ta stawon watanni 3.