'Yan ta'addar Boko Haram sun kashe manoma 110 a harin da suka kai a jihar Borno da ke arewa maso-gabashin Najeriya.
Babban Jami'in Aiyukan Jin Kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Edward Kallon ya bayyana cewar, 'yan ta'addar sun kaiwa manoma hari a kauyen Garin Kwashebe a ranar Asabar din karshen makon da ya gabata.
Kallon ya bayyana cewar an kashe manoman shinkafa 110 tare da jikkata wasu da dama sakamakon harin, inda ya ce "Wannan harin na da ban tsoro. Ina mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda aka kashe. Ina fatan samun jin kai ga wadanda suka jikkata."
Kallon ya kuma ce, an yi garkuwa da mata da yawa a yayin kai harin, kuma gwamnati na ta kokarin kwato wadanda aka sace.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya la'anci harin inda ya ce "Wannan mummunan aiki ya jikkata dukkan kasar."
A gefe guda, labaran da jaridun Najeriya suka fitar sun ce mutane 44 aka kashe a harin.