Gwamnan lardin Janar Toke Dadi ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, a ranar lahadin data gabata ne makiya suka kai hari garin Nya Pende da ke da nisan kilo mita dari 6 kudu da babban birnin ƙasar N’Djamena.
Ya ce bayaga waɗanda suka rasa ransu, akwai kuma mutum 9 da suka samu raunuka biyar daga cikinsu harbin bindiga ne.
Tuni dai gwamnatin ƙasar ta aike da sojoji ƙimanin motoci 20 don bin bayan maharan.
Kawo yanzu dai ba a san dalilin faruwar lamarin ba, sai dai Dadi ya ce ana iya danganta lamarin da kashe wani manomi a ranar 30 ga watan Nuwamba, lamarin da ya sa jama’ar kauyen suka kai hari a wuraren kiwo, inda suka kashe wani dattijo da dabbobi da dama.
Rikici tsakanin makiyaya da manoma ya zama ruwan dare a kan iyakar Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI