Rahotanni daga Sudan na cewa ya zuwa yanzu jimillar mutane 103 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a kasar.
Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida na cewa tsawon 'yan watanni kenan ake ta tafka ruwan sama a Sudan, wanda ya janyo ambaliyar ruwan da ta sake yin ajalin mutum 1.
Hakan ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa mutane 103.
Mutane 50 sun jikkata sakamakon ambaliyar ruwan, gidaje dubu 69,551 sun samu matsala ko sun rushe baki daya.
Ma'aikatar ta kuma ce, a jihohi 16 daga cikin 18 da aka samu mamakon ruwan saman, sama da kadada dubu 4 na amfanin gona ya lalace, yayinda sama da shanu dubu 5 kuma suka mutu.
Ofishin Wakilin Din-Din-Din na Sudan a Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga hukumomin kasa da kasa da su taimakawa yankunan da ibtila'in ya shafa.
Ma'aikatar Kula da Albarkatun Ruwa da Ban Ruwa ta Sudan ta bayyana cewar kogin Nil ya yi cikar da ba a taba gani ba a shekaru 100 da suka gabata.
Majalisar Tsaro ta Sudan ta aiyana dokar ta baci ta tsawon watanni 3 sakamakon ambaliyar ruwan.