Adadin mutane 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai kwanakin da suka gabata a Jamhuriyar Nijar.
Bayanan farko da aka fitar sun bayyana cewar, mutane 56 ne suka mutu, wasu 20 suka jikkata sakamakon hare-haren da 'yan ta'adda suka kai a kauyukan Tchombangou da Zaroumdareye da ke Nijar.
Shugaban da ke kula da kauyukan Almou Hassane ya shaida cewa, a kalla mutane 100 ne suka mutu sakamakon hare-haren da aka kai musu.