An sanar da cewa mutane 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon rushewar wata mahakar zinare a Kamaru.
Mutane 6 kuma sun jikkata a hatsarin da ya afku a mahakar ma'adanan da ke yankin Kambele.
An bayyana cewa masu hakar ma'adanan na aiki ba bisa ka'ida ba a mahakar.
Hadarin da ke haddasa mutuwa na yawan faruwa a mahakar ma'adinai da ke yankunan arewa da gabashin kasar.
Dangane da bayanan ma'aikatar ma'adinan ta Kamaru, kusan mutane 50 ne suka rasa rayukansu a kusan hatsarin hakar ma'adinai 20 a cikin shekaru biyu da suka gabata.