Cutar murar tsuntsaye ta bulla a Sanagal, wanda hakan ya sanya mutuwar tsuntsaye 750 a arewacin kasar.
Ministan Muhalli Abdou Karim Sall ya shaida cewa, a ranar 23 g Janairu tsuntsaye 750 sun mutu a Filin Shakatawa na Djoudj da ke yankin Saint Louis.
Sall ya sanar da cewar, an rufe filin shakatawar tare da dakatar da ziyartar sa, kuma cutar na iya yaduwa cikin gaggawa saboda ana cikin yanayi da tsuntsaye suke sauya matsugunai a kasar.
Filin Shakatawa na Djoudj na cikin jerin wuraren tarihi na Hukumar UNESCO, wajen na da girman hekta dubu 16, kuma akwai nau'ikan tsuntsaye 400 da ke rayuwa a ciki.
A ranar 23 ga Janairu ne aka ga tsuntsaye 750 sun mutu a filin inda tuni aka aike da su zuwa asibit, don gano musabbabin mutuwar su.