Babban Sakataren Hukumar da ke kula da Tafkin Chadin, Ambassada Mamman Nuhu ya ce za su ci gaba da aiwatar da shirin zaman lafiyar ta hanyar haɗin kai da ƙungiyoyin fararen hula waɗanda ya ce suke taimakawa gaya wajen tabbatar da zaman lafiyar, ya yin da yake tsokaci dangane da taron gwamnonin jihohin da suka kewaye Tafkin a Najeriya.
Ambassada Nuhu ya ce shirin da suke ƙaddamarwa ya kai ga mutane miliyan 1,357,713 cikin su harda mata dubu 726,222 ta hanyar samar musu da tsaro domin gudanar da harkokin su na yau da kullum wanda ya dangata shi da haɗin kan mutanen da ke yankin.
Wata daga cikin waɗanda suka gudu daga kauyukan su na Fouli, Hadje Abderahmane mai shekaru 37, ta ce wannan rikici na Boko Haram ya raba su da hanyoyin da suka saba rayuwar yau da kullum, abinda ya sa ta tsere zuwa Bol inda yanzu haka ta samu mafakar da take samun kula da kuma sanya ƴaƴan ta a makaranta.
Taimakin shugaban Najeriya Kashim Shattima da babban sakataren Hukumar da ke kula da Tafkin Chadin, Ambassada Mamman Nuhu tare da gwamnonin yankin a wajen taron da suke gudanarwa. © Nigerian PresidencySu ma hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya irin su UNDP da UNHCR a Lardin Lac da ke ƙasar Chadi sun taimaka wajen samarwa mutane 981 katin shaida da kuma samar musu da kayan more rayuwa a Koulkime, yayin da UNDP da WFP kuma suka ƙaddamar da shirin bai wa yara abinci a makarantun da aka gyarar azuzuwan su, wanda ya kai ga dalibai 362 sun ci gajiyar shirin, kuma 171 daga cikin su mata ne.
Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da Afirka, Ahunna Eziakonwa ta bayyana cewar ƙaddamar da shirin SMDF da NFF domin kai ɗauki ga jama'ar da ke yankin Tafkin Chadi, ya taimaka sosai ta hanyar sauya rayuwar jama'ar da rikicin Boko Haram ya shafa da inganta shi.
Jami'ar ta ce tuni shirin ya samu goyan bayan abokan huldar su sosai ciki harda gwamnatocin ƙasashen Jamus da Sweden.
Sanarwar da Scheherazade Bouabid, babban jami'in yada labaran shiya na UNDP da ke kula da Yammaci da Tsakiyar ƙasashen Afirka ya rabawa manema labarai ,ta ce shirin da suke ya shafi ɗaukacin ƙasashen Takin Chadi, kuma sama da mutane miliyan 6, ciki harda ƴan gudun hijira da waɗanda suka koma gidajen su ne ke samun tallafi domin sake gina rayuwarsu a yanki.
Wannan taron da gwamnatin Jihar Yobe ke ɗaukar nauyi, na samun goyan bayan Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU da kuma gwamnatin Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI