Mutane 19 sun rasa rayukansu sakamakon fadawa wani kogi da wata motar haya ta yi a Zambiya.
Jami'in dan sanda na yankin Mungwi da hatsarin ya afku Jestus Nsokolo ya bayyana cewa, motar na dauke da masu sana'ar sayar da wayar hannu su 57.
Ya ce, a kalla mutane 19 ne suka mutu sakamakon hatsarin, kuma hatsarin ya afku sakamakon gudun wuce sa'a da daukar mutane da kaya sama da kima da aka yi.
An bayyana kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin Chambeshi da ke yankin.