Motocin kayan agaji sun fara isa yankin Darfur, bayan sahalewar sojojin Sudan

Motocin kayan agaji sun fara isa yankin Darfur, bayan sahalewar sojojin Sudan

Iyakar Adre ta Chadi itace mafi kusa da isa Darfur, kuma sojoji da kuma abokan rikicin nasu da mayakan RSF sun hana shigar da kayan agaji cikin watanni 16 da aka kwashe ana tafaka yakin.

A wata Fabrarun da ya gabata ne gwamnatin sojin ƙasar ta bada umarnin dakatar da shigar da kayan agaji ta wannan mashigin a hukumance, tana mai cewa dakarun na RSF na samun makamai ta wannan iyaka.

Hukumar bada agajin gaggawa ta majalisar ɗinkin duniya a Sudan ta bakin shugabanta Justin Brady ta ce zuwa yanzu manyan motoci 15 ne suka isa yankin na Darfur cikin guda 131 da ke kan iyakar suna jiran umarnin shiga.

A wata sanarwa da hukumar samar da abinci ta majalisar ɗinkin duniya ta fitar ta ce kayan abincin da suka sami damar shiga yankin sun haɗar da man girki, shinkafa, Dawa, da sauransu, kuma ana sa ran zasu ishi mutane dubu 13.

Hukumar ta ce tana fatan sojojin zasu bada damar shigar da dukannin kayan abincin da ta tanada wadanda zasu ishi mutane akalla dubu 500

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)