Moroka ta yi wa manoma tabar wiwi ba bisa ka'idaba kusan dubu 5 afuwa

Moroka ta yi wa manoma tabar wiwi ba bisa ka'idaba kusan dubu 5 afuwa

Ma’aikatar shari’a ta kasar ce ta sanar da wannan afuwa a jajibirin bikin ranar da Moroko ta samun ‘yancin kai, inda ya ce Mai Alfarma Sarki Muhammad na 6 ne ya dauki  wannan mataki saboda dalilai irin na jinkai.

Wasu daga cikin wadannan mutane dubu 4 da 831, tuni aka yanke musu hukuncin dauri a gidan yari bayan an tabbatar da laifukansu, yayin da ake gudanar da bincike a kan wasu, bisa dalilan cewa sun mallakin manyan filaye da ake gudanar da noman tabar wuiwui a cikinsu, duk da cewa noman wannan ganye ba da izini ba, abu ne da ya saba wa dokokin kasar.

Moroko ta fi kowa nomar ganyen wuiwui

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, Mokoro ce kasar da ta fi kowace noman wannan ganye a duniya, tun bayan da mahukuntan kasar suka amince da dokar da ke bayar da damar yin hakan a shekara ta 2021 amma a karkashin kulawar hukuma.

Wasu alkaluma da aka fitar a shekara ta 2019, sun tabbatar da cewa sama da iyalai dubu 120 ne suka dogara noman wannan tabar a matsayin hanyar samun abinci, kuma duk da cewa akwai tsauraren dokoki da hukunta wanda aka sama da laifi, amma jama’a sun ci gaba da wannan sana’a har zuwa lokacin da aka halasta ta a wasu yankuna cikin shekara ta 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)