Mnangagwa ya karɓi jagorancin SADC yayin taron zaman lafiyar kudancin Afrika

Mnangagwa ya karɓi jagorancin SADC yayin taron zaman lafiyar kudancin Afrika

Taron na wannan karo ya mayar da hankali ne a game da samar da zaman lafiya a cikin kasashen yankin, musamman ma lura da yadda ake kara shiga zaman tankiya da kuma zargi a tsakanin Congo da Rwanda, saboda yakin da ake gwabaza wa a gabashin Congo. 

Duk da cewa babu wani matakin da taron ya dauka game da wannan batu, amma sanarwar da shugabannin suka fitar ta ce za a ci gaba da kokari don samar da zaman lafiya kan iyakokin kasashen biyu, yayin da a hannu daya shugabannin suka lashi takobi daukar kwararran matakai domin shawo kan cutar kyandar biri, wadda tuni ta shiga a tsakanin al’ummominsu. 

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun kira ga shugabannin yankin domin su ja hankalin takwaransu Emmerson Mnangwagwa dangane da yadda yake cin zarafin ‘yan adawa, to amma duk da haka, a karshe dai taron ya zabi Mnangwagwa a matsayin wanda zai ci gaba da rike ragamar jagorancin kungiyar ta SADC tsawon shekara daya mai zuwa. 

Wani abu da aka lura da shi a wannan karo shi ne rashin halartar shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema, abin da ya kara fitowa fili karara da tsamin dangantar da ke tsakaninsa da Zimbabwe tun daga lokacin da shugaban ya kulla yarjejeniyar soji da Amurka.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)