Kasar Misira ta bayyana sakawa al'umman kasashen Larabawa dake neman shiga kasar dokar karbar visa.
Dokar ba za ta hada da kasashen dake da yarjejeniyar shiga ba visa da kasar ta Misira ba.
Ministan harkokin cikin gidan Masar Mahmud Taufik ya sanar da dokar mai lamba sakin layi 380.
Dokar ta bayyana kuma za'a fara amsar kudaden visa ga dukkanin 'yan kasashen Larabawa dake neman ziyarar Misira amma banda wadanda kasarsu keda yarjejeniyar ziyarar juna da Misira ba tare da visa ba.
Duk da dai ministan bai bayyana kasashen dake da yarjejeniyar da Misira akan rashin karbar visa ba, Misira a watan Nuwamban shekarar 2017 ta fara neman 'yan kasar Katar dake neman ziyarar kasar karban visa, haka kuma a watan Yunin shekarar 2020 ta sakawa 'yan kasar Saudiyya, Haddadiyar Daular Larabawa, Kuwait, Bahrain da Umman karbar visa gabanin ziyararta.