Ministan Tsaron Turkiyya Akar na ziyara a Libiya

Ministan Tsaron Kasa na Turkiyya Hulusi Akar tare da Shugaban Rundunar Sojin Kasar Janaral Yasar Guler na ziyara a Libiya.

Akar da Janaral Guler sun je Libiya don yi nazari karkakashin yarjejeniyar atisaye da aka kulla.

Bayan faretin soji na sannu da zuwa da aka yi wa Akar da Guler, sun tafi zuwa Sansanin da aka samar don bayar da horo da tsaro na hadin kai a yayin atisayen.


News Source:   www.trt.net.tr