Miliyoyin yara kanana ba sa iya zuwa makaranta a Afirka sakamakon annobar Corona da rikice-rikice a nahiyar.
Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Save the Children ta yi kira ga Hukumomin da Gwamnatoci da su samar da yanayin da yara kanana za su samu damar zuwa makaranta.
Sanarda da Kungiyar ta fitat ta ce, "Sakamakon annobar Corona da rikice-rikice yara kanana ba sa iya zuwa makaranta a Afirka."
Sanarwa ta ce sakamakon wannan yanayi ilimi na samun koma baya, a saboda haka aka yo kira da a magance wannan matsala.
A yankunan da qke saka yara kana aikatau kuma, 1 daga cikin dukkan yara kanana 5 yana aikin karfi.