Binciken da kamfanin dillancin Labarai na Reuters ya yi, ya gano yadda ayyukan kungiyoyin ta’addanci ke ƙaruwa a yankin babu ƙaƙƙautawa a ƴan shekarun nan.
Yankin na Afrika maso yamma na fuskantar ƙaruwar ayyukan ta’addanci da muggan hare-hare, kuma hakan na cikin dalilan da binciken kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi wuƙar ƙugu da su wurin gano yankin ya zama dandalin ƴan ta’adda.
Ko a ranar 17 ga watan Satumbar da muke ciki mayaƙan jahadi sun ƙaddamar da wani mummunan hari a Bamako babban birnin ƙasar Mali, inda suka hallaka gwamman ɗalibai a makarantar ƴan sanda tare da kewaye filin jirgin sama da kuma bankawa jirgin shugaban ƙasar wuta.
Yankin na Sahel na fuskantar ta’addanci dake da alaƙa da kungiyoyin Alqa’ida da IS, kuma hakan ya yi sanadin kashe dubban jama’a da raba miliyoyi da mahallansu.
Wasu alƙaluma da Reuters ta samu daga wata gamayyar masu bibiyar wuraren da rikice-rikice ya shafa ta Amurka ya gano cewar adadin ayyukan ƴan ta’adda ya kusa ninkawa a ƙasashen Burkina Faso da Mali da Niger tun daga 2021. Addadin na kaiwa 224 duk wata daga 128 da yake a baya.
Tashin hankalin da yankin ke fuskanta ya taimaka wurin ƙaruwar ƴan gudun hijira daga Afirka ta yamma zuwa nahiyar turai. Masu shiga turai daga Afirka sun ƙaru zuwa kaso 62 a watanni 6 na farkon 2024.
Wurare da dama na ƙarƙashin ƴan ta’adda da masu iƙirarin jihadi, abinda ke ƙara jefa fargaba kan yuwuwar yankin ya zama sansanin horon ƴan ta’adda da kuma kitsa hare-hare a manyan birane da maƙwaftan ƙasashe harma da ƙasashen yamma.
Ana ganin ayyukan ta’addancin sun taimaka wurin haddasa juyin mulki a Burkina Faso da Mali da Nijar, abinda ya sa ƙasashen ke neman haɗin gwiwa da ƙasar Rasha.
Ƙarfin ƙasashen yamma ya ragu a yankin, musamman bayan korar sojin Amurka daga sansaninsu dake dake Nijar abinda ya bar wani gagarumin gibi wurin kula da tsaron sararin samaniya a yankin.
A wata magan da Janaral Michael Langley shugaban dakarun sojin Afirka dake kula da nahiyar Afirka yayi wata guda d aya gabata ya ce dukkanin ƙungiyoyin na da wani buri na kaiwa Amurka hari, to sai dai wasu jami’ai da ƙwararru na ganin cewar kungiyoyin ba su da wani buri na kaiwa Amurka hari.
Wani tsohon jami’in hukumar leƙen asirin Amurka CIA Will Linder ya ce harin da aka kai Bomako da Barsalogho ya nuna cewar ƙoƙarin da shugabannin sojin ƙasashen Mali da Burkina Faso ke yi ya gaza, don haka akwai buƙatar ƙasashen su sauya salo da dabarun tunkarar yadda za’a daƙile ayyukan masu iƙirarin jihadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI