MDD ta yi gargaɗi a kan hare-haren martani kan fararen hula a Sudan

MDD ta yi gargaɗi a kan hare-haren martani kan fararen hula a Sudan

Rundunar sojin Sudan, wadda ke yaki da dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF tun daga watan Afrilun shekarar 2023, ta kutsa cikin jihar Al-Jazira a makon da ya gabata, inda su ka sake kama babban birnin jihar, Wad Mdani daga hannun RSF ɗin.

Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun ruwaito yadda mayaƙan sa-kai da ke taimaka wa sojoji su ka jagoranci hare-haren da ke da nasaba da ƙabilanci a kan ƴan tsirarrun al’ummomi a jihar, inda su ka kashe mutae 13 ciki har da ƙananan yara 2.

Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam a yankin, ta cikin wani rahoto, sun ce mazauna ƙauyen Kanabi da wasu manoma daga sauran sassan Sudan sun haɗa kai da mayaƙan RSF, waɗanda su ka yi iko da Al-Jazira tsawon shekara guda.

A wannan Laraba, ma’aikatan harkokin wajen Sudan ta Kudu, wadda ta ɓalle daga Sudan a shekarar 2011 ta ce an kashe ƴan ƙasarta da dama a kan iyaka biyo bayan sake karɓe iko da Wad Madani.

Ana zargin ssojin ƙasar da dakarun RSF da aikata laifukan yaƙi, ciki har da kisan fararen hula, da kuma harbi kan mai uwa da wabi a kan yankunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)