MDD ta bayyana takaicinta kan yadda aka mayar da Afirka cibiyar ta'addanci

MDD ta bayyana takaicinta kan yadda aka mayar da Afirka cibiyar ta'addanci

Mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar, Amina J. Muhammad, wadda ke bayyana wannan takaicin, lokacin da take gabatar da jawabi ga kwamitin sulhu na Majalisar, ta bayyana ta’addanci a matsayin babbar barazana ga zaman lafiya da ya mamaye nahiyar Afirka.

Ta ce wannan kalubale ya haifar da illa mai munin gaske ga shirin samar da ci gaba mai dorewa  a nahiyar.

A cewar mataimakiyar magatakardar, yankin Kudu da Hamadar Sahara na dauke da kusan kashi 59 cikin 100 na mace-macen da ke da nasaba da ayyukan ta’addanci a duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yankin Sahel ne kan gaba wajen fama da yake-yake mafiya muni, tare da kiyasin sama da mutum 6,000 ne suka mutu sakamakon hare-haren ta’addanci cikin shekaru ukun da suka gabata.

Burkina Faso ce kan gaba da yawan mace-mace saboda ta'addanci, inda ta samu karuwar kashi 68 na adadin wadanda aka kashe, wanda hakan Majalisar ta ce baya rasa nasaba da karancin taimako da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)