Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa game da halin da mutane ke ciki a yankin Tigray da sojojin gwamnatin Itopiya da dakarun yankin suke fafata rikici.
Sanarwar da Kwamitin Tsaron na MDD ya fitar ta ce, "Muna matukar damuwa da dimauta game da labaran samun fyade da aiyukan keta hakkokin dan adam a yankin."
Sanarwar ta bayyana gargadin Kwamitin game da arangamar da aka dauki tsawon watanni 6 ana yi.
Sanarwar ta tabo batun sojojin Eritiriya da suka hada kai da na gwamnatin Itopiya tare da shiga yankin Tigray.
A makon da ya gabata Mataimakin Kwamitin Aiyukan Jin Kai na MDD Mark Lowlock ya bayar da bayanai ga Kwamitin Tsaron kan halin da ake ciki a Tigray inda ya ce duk da sanarwar da Itopiya ta fitar na ta janye, amma dakarun Eritiriya na ci gaba da zama a yankin.
Lowlock ya kuma ce, daga cikin mutane miliyan 6 da ke yankin, miliyan 4,5 na bukatar taimakon gaggawa, sannan an samu fyade da dama da masu kayan sarki suke da hannu a aikatawa.