MDD ta amince da kashe dala miliyan 40 don yaki da Ebola a Kongo

MDD ta amince da kashe dala miliyan 40 don yaki da Ebola a Kongo

Asusun Aiyukan Gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da a kashe dala miliyan 40 don yaki da cutar Ebola da ta sake bayyana a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Kuma Babban Jami'in Kula da Asusun Mark Lowcock ya shaida cewar sakamakon ganin yadda cutar ke karuwa a Kongo ya sanya an ware karin dala miliyan 40 don yakar cutar.

Lowcock ya ce za a yi amfani da kudin taimakon don karfafa tsarin kula da lafiya a kasar.

A ranar 1 ga watan Yuni Ministan Lafiya na Kongo Eteni Longondo ya ce akwai sabbin mutane da suka kamu da cutar Ebola a yankin Mbandaka na arewa maso-yammacin kasar, kuma 5 daga cikinsu sun mutu.

A watan Agustan 2018 Ebola ta bulla a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, kuma ya zuwa yau ta yi ajalin mutane dubu 2,025 daga cikin dubu 314 da ta kama.


News Source:   www.trt.net.tr