MDD na zargin Dubai da safarar makamai zuwa Sudan

MDD na zargin Dubai da safarar makamai zuwa Sudan

Majalisar ta samu waɗannan bayanai ne ta hanyar  wasu kafofin tara bayanan yaƙi da kuma wasu hotuna da aka samu ta tauraron ɗan’adam.

Wasu rahotanni na Kamfanin Dillancin Labari na Reuters sun nuna a kalla jirage 86 daga Hadaddiyar Daular Larabawa ne suka nufi wani filin jiragen sama a Amdjarass da ke gabashin Chadi tun bayan ɓarkewar yakin a watan Afrilun shekarar 2023, da zummaer kaiwa mayaƙa makamai a Libya.

Hadaddiyar Daular Larabawa, wacce ke zama babbar ƙawa ga kasashen Yamma a yankin Gabas ta Tsakiya, ta musanta zargin da aka yi mata inda take cewa ta na aika kayan agaji ne zuwa Sudan ta Chadi, amma ba makamai ba.

Kasar ta kuma yi watsi da rahoton da Kwamitin Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar tun a watan Janairu, wanda ya zarge ta da samar da kayayyakin soji ta tashar jirgin saman Chadi ga rundunar kai ɗaukin gaggawa, da ke yaki da sojojin Sudan a rikici da ya barke a tsakaninsu.

Rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubun dubatar mutane da jikkata wasu da dama tare da raba wasu da dama da matsugunasu.

Wasu hotunan bidiyo da ba a tantance ba da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi bitar daga Amdjarass da aka ɗauka a wannan shekara, yana nuna wasu shaidu guda biyu da aka samu a kan hanya da aka jibge dauke da akwatunan khaki, wadda wasu daga cikinsu ke ɗauke da alamar tutar haɗaɗɗiyar daular larabawa..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)