Gargɗin shugaban Hukumar Kare Hakkin dan Adam na Majalisar, Volker Turk, ya azo ne kwana guda, bayan da shirin hukumar abinci ta duniya ya dakatar da aikin bayar da abinci na wucin gadi a Sudan ɗin.
Rahoton Majalisar ya bayyana cewa, Sudan na dab da faɗawa wani ƙazamin yaƙin, abin da ke nuna fargabar ɓarkewar tsananin yunwa, da kuma ƙaruwar laifukan yaƙi da asarar ɗimbin rayuka.
Volker Turk ya shaidawa taron Hukumar Kare Hakkin dan Adam a Geneva cewa, za a fuskanci barazana mai munin gaske da ba a taɓa gani a ƙasar ba.
A watan Afrilun 2023 ne, yaƙi ya ɓarke a ƙasar tsakanin masu fafutukar kujerar mulki, wato shugaban mulkin soji Janar Al-Burhan, da kuma tsohon mataimakinsa wanda ke jagorantar dakarun kai ɗaukin gaggawa da suka rikiɗe zuwa ‘yan tawayen RSF.
Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewa, tsananin yunwa ya fantsama a yankuna biyar na ƙasar Sudan din, ciki kuwa har da kwararar ‘yan gudun hijira a yankin Darfur.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI