Wannan yaki da ake fama da shi a Sudan, yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, yayin da a hannu daya MDD ke cewa shi ne rikici mafi muni wajen haifar da cikas ga masu ayyukan jinkai a wannan zamani.
Duk da cewa yakin ya shafi mafi yawan jihohin kasar ta Sudan, amma fararen hula a El-fasher mai kunshe da mutane sama da milyan biyu a yankin Darfour, na daya daga cikin wadanda suka fuskantar kuncin rayuwa saboda yadda ‘yan tawaye suka yi masa kofar-rago.
Wasu daga cikin dakaru dake fada da juna a yankin El Facher © APRikicin na Sudan dai na daga cikin batutuwan da za su fi daukar hankula a lokacin wannan taro na MDD, yayin da wasu ke ganin cewa lokaci ya yi domin sasanta shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar janar Abdel Fattah al-Burhan da abokin hamayyarsa Janar Mohamed Hamdan Daglo.
Babban magatakarda na MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar damuwa a game da halin da fararen hula suka tsinci kansu a Sudan, inda ya yi kira ga bangarorin biyu da su tsagaita wuta tare da shiga tattauna domin sulhu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI