Mata, maza da yara ne suka bazama kan titunan garin a matsayin martani ga kutsen da ƴan bindiga suka yi a gari amakon da ya gabata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 3, waɗanda ƴan ta’addan suka yi wa yankan rago.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar da ya bayyana dalilin fitowar su cikin fushi ta cikin wani hoton bidiyo, ya ce ƴan ta’addan su na yi musu kutse cikin birnin, inda su ke kashe iyaye, matansu da ƴaƴansu.
Dubban mutane ne suka arce daga wasu sassan birnin da ɗan kayayyakin da za su iya ɗibawa, biyo bayan wa’adin da wata ƙungiyar ƴan ta’adda ta ɗibar musu.
Hotunan da aka wallafa a shafukan dandalin sada zumunta sun nuna ɗimbim mutane a ruɗe su na barin birnin a ƙasa da jakuna.
Wasu mazauna birnin sun ce ƙungiyar ƴan ta’addan ta bai wa al’ummar su koma yankuna na 7,8 da 9 na Djibo. Amma waɗannan yankuna sun kasance a ƙarƙashin ikonsu tsawon shekara guda, amma a maimakon haka sai su ka nufi sansanin soji kai tsaye a cewar majiyoyi da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI