Mayakan sa kai sun kashe fararen hula sama da 50 a arewa maso gabashin Congo

Mayakan sa kai sun kashe fararen hula sama da 50 a arewa maso gabashin Congo

Rahotanni na cewa, mayaƙan ƙungiyar sa-kai ta CODECO da ke iƙirarin kare muradun ƙabilar Lendu ta Manoma ne suka kai hari kauyuka a Djaiba, mai ɗauke da wani sansanin ƴan gudun hijira a lardin Ituri.

Shugabar sansanin Antoinnette Nzale ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa fararen hula 55 ne suka mutu, kuma adaɗin na iya ƙaruwa , saboda ana ci gaba da zakulo gawarwakin daga gidajen da aka kona.

Tun farko, Basaraken ƙauyen Djugu, Jean Vianney ya ce harin ƴan bindigar ya kashe mutane 35 izuwa safiyar talata, bayaga waɗanda suka samu raunuka da kuma asarar dukiyar da aka tabka.

Alƙaluman Cibiyar Nazarin da Bincike kan ta'addanci, sun nuna cewa, hare-haren ƙungiyar CODECO sun kashe kusan mutane 1,800 tare da raunata fiye da 500 a cikin shekaru hudu, wato daga 2022.

Sama da ƙungiyoyi 120 masu ɗauke da makamai ne ke fafatawa a gabashin Jamhuriyar Demokradiyar Congo, waɗanda galibinsu ke neman filaye dan sarrafa ma'adinai, yayin da wasu ke ƙoƙarin kare al'ummominsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)