Mayakan JNIM sun ɗauki alhakin harin Barsalogho a Burkina Faso

Mayakan JNIM sun ɗauki alhakin harin Barsalogho a Burkina Faso

Kungiyar mai da'awar kare Muslunci da Muslumai ta dauki alhakin kai harin ne ta cikin wani faifan bidiyo da ta yada a shafinta na farfaganda, inda a ciki ake iya ganin gomman gawarwaki shinfide cikin ganuwa.

A cewar wasu shaidun gani da ido, ‘yan ta’addar sun kaddamar da harin ne da sanyi safiyar Asabar daidai lokacin da dakarun Burkina Faso ke tsaka da gina ganuwa domin kare kan su tareda gudun mawar wasu mazauna gari.

Majiyar ta kara da cewa an cigaba da kai harin har  karfe hudun yamma hakan ne ya sanya ‘yan ta’addan yin harbin harbin kan mai uwa dawabi.

Kawo yanzu babu wasu alkalumma a hukumance da gwamnatin ta fitar gameda harin, sai dai a acewar wasu majiyoyin tsaro da na ‘yan kungiyar sa kai, harin da aka kai a Barsalogho ya lakume rayukan  mutune 300 tareda jikkata wasu sama da 200.

Gwammnatin Burkina Faso ta bakin kakakin ta Rimtalba Jean Emmanuel, ta kira harin da na marasa imani tareda shan alwashin yin ramako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)