Mayakan Haftar sun kashe fararen hula 5 a Tarabulus

Mayakan Haftar sun kashe fararen hula 5 a Tarabulus

Fararen hula 5 ne suka rasa rayukansu sakamakon hari da makamin roka da 'yan tawaye mabiya dan juyin mulki Haftar Khalifa suka kai a Tarabulus Babban Birnin Libiya.

Babban Sakataren Ma'aikatar Lafiya ta Libiya Amin Al-Hashimi ya shaida cewar 'yan tawaye mabiya Haftar sun kai hari da makamin roka a Tarabulus Babban Birnin Kasar.

Hashimi ya kara da cewar makamin rokar da aka harba ya fado kan gidajen fararen hula a yankin Suk Al-Sulais da ke Tarabulus, kuma ya kashe fararen hula 5.

Hashimi bai bayar da bayanai game da wadanda suka samu raunuka ba sakamakon harin.

Tun watan Janairu zuwa yau mayakan Haftar suke kai hare-hare kan gidajen fararen hula a Tarabulus inda suke kashewa tare da jikkata daruruwan mutane da suka hada da mata da yara kanana.


News Source:   www.trt.net.tr