Gwamnatin Libiya da ke Kai Farmakan Fushin Dutse Mai Aman Wuta ta sanar da cewar mayakan Haftar da ke sansanin Watiyya a kudancin Tarabulus Babban Birnin Kasar sun fara mika wuya ga sojojinta.
Sanarwar da Ofishin Kai Farmakan ya fitar ta ce wasu mabiya Haftar 6 sun mika wuya ga Kwamandan yankin Manjo Janar Usama Juwaili.
A ranar Talata ne gwamnatin Libiya ta fara kai farmakai don kwace sansanin na Watiyya inda ta yi wa yankin gaba daya kawanya.