'Yan tawayen Libiya da ke biyayya ga dan juyin mulki Haftar Khalifa sun kai harin bam da safiyar ranar Sallah kan filin tashi da saukar jiragen sama na Mitiga da ke Tarabulus Babban Birnin kasar.
Ofishin Yada Labaran Farmakan Bacin Ran Dutse Mai Aman Wuta da dakarun gwamnatin Libiya ke kaiwa ya bayyana cewar 'yan tawayen na Haftar da sanyin safiyar ranar Sallah sun kai hari da makaman roka kan filin tashi da saukar jiragen sama na Mitiga.
Sanarwar ta ce mayakan na Haftar sun nuna rashin daraja da girmamawa ga Azumin watan Ramadhan da kuma bukukuwan Sallah da Musulmi suke yi.
Sanarwar ba ta bayana ko an samu asarar rayuka ko dukiya ba sakamakon harin.
A gefe guda kuma wasu fararen hula 2 sun rasa rayukansu a lokacin da suke komawa gida sakamakon fashewar wani bam da 'yan tawayen na Haftar suka binne a gefen hanya a kudancin Tarabulus Babban Birnin Libiya.
Kakakin rundunar sojin Libiya Kanal Muhammad Kununu ya ce jami'ansu suna ci gaba da aiyukan kwance bama-baman da 'yan tawayen Haftar suka binne, kuma suna kira ga jama'a da kar su komwa gidajensu har sai an ba su sanarwar hakan.