Mayakan Haftar a Libiya sun fara sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta

Mayakan Haftar a Libiya sun fara sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta

Sojojin Libya sun sanar da cewa wasu dakaru masu biyayya ga Khalifa Haftar, shugaban haramtattun dakaru a gabashin kasar, sun kashe wani mutum a garin Sevkene dake yankin Al-Jufra.

Kakakin sojojin a yankin Jufra a Libya Abdulhadi Dirah ya bayyana cewa mayakan sa kai na Haftar sun kashe wani saurayi mai suna Ali Muhammed Juma.

Dirah ya lura cewa mutane sun fara taruwa a yankin inda lamarin ya kasance cikin mawuyaci.

Sojojin Libya sun sanar da cewa jiragen yakin da ke da alaka da Khalifa Haftar sun keta yarjejeniyar tsagaita wutar.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa daga Cibiyar 'Yan Jaridu ta Operation Fushin Dutsen Volcano an bayyana cewa, an lura da wani jirgin yaki da helikwafta da ke alaka da Haftar a sararin samaniyar El-Jufra, kilomita 600 kudu maso gabashin Tripoli.

Sakamakon taron hadin gwiwar kwamitin soja na 5 + 5 da aka gudanar a Geneva, Switzerland, a ranakun 19-23 ga watan Oktoba, an sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta na dindindin tsakanin gwamnatin Libya da wakilan da ke da alaka da Haftar.


News Source:   ()