Dakarun Sojin Gwamnatin Sulhun Kasa ta Libiya sun bayyana cewar sun lalata motocin yaki mallakar 'yan tawayen Haftar Khalifa dan jyin mulki a kudancin Tarabulus Babban Birnin kasar, sun kuma fatattaki 'yan tawayen daga yankunan Kazirma da Ahyaul Barriyya wanda yanki ne mai muhimmanci.
Kakakin Rundunar Sojin Libiya Kanal Muhammad Kununu ya fitar da rubutacciyar sanarwa inda ya ce dakarunsu sun lalata motocin yaki na Haftar guda 10.
Kununu ya kara da cewar sun kuma kwace yankunan Kazirma da Ahyaul Barriyya da ke kudancin Tarabulus.