Mayaƙan M23 sun kwace ikon birnin Bukavu da ke gabashin Congo

Mayaƙan M23 sun kwace ikon birnin Bukavu da ke gabashin Congo

A baya dai birnin na Bukavu mai mutane miliyan ɗaya, ya kasance ƙarƙashin kulawar dakarun gwamnatin Congo, kuma kwace shi da ƴantawauen M23 suka yi a yanzu, ya basu damar mamaye yankin Kivu, bayan kwace birnin Goma a ƙarshen watan Janairun da ya gabata.

Tun a ranar Juma’ar data gabata ne dai sojojin Congo suka tsere daga birnin, tare da barin wasu daga cikin makamansu.

Ƙasashe na ci gaba da yin kiraye-kiraye ga Rwanda da ta daina goyon bayan mayaƙan M23, duk da cewa ta sha musanta zargin da ake yi cewar sojojinta na taimaka musu a cikin Congo.

Wakilin Kamfanin Dillancin Laraban Faransa AFP ya ruwaito cewar, a lokacin da mayaƙan suka shiga cikin birnin na Bukavu, mutanen garin sun yi cincirindo a kan hanyoyi suna jinjina musu.

Rahotanni sun nuna cewar wasu daga cikin mazauna garin, sun buƙace mayaƙan na M23 su ci gaba da matsawa har sai sun shiga cikin babban birnin ƙasar Kinshasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)