An ƙaddamar da farmakin ne a ranar 9 ga watan Agustan nan a ƙauyen Tawori da ke yankin gabashin Burkina Faso kamar yadda gwamna Ram Joseph Kafando ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar jim kaɗan da ziyarar da ya kai wani asibiti da ke kula da waɗanda suka samu rauni a harin.
Kodayake gwamnan bai bayar da adadin mutanen da suka samu raunin ba, sannan bai ce komai ba kan ko sojoji na cikin waɗanda suka mutu ko jikkata.
Gwamnan ya jinjina wa jami’an kiwon lafiyar da ke kula da majinyatar saboda kokarinsu.
Burkina Faso da makotanta Mali da Nijar sun jima suna yaƙi da mayaƙa masu iƙirarin jihadi da suka bazu a yankin Sahel da ke yammacin Afrika.
Gazawar gwamnatocin da suka gabata a waɗannan ƙasashen ne ta tilasta wa sojoji juyin mulki har sau biyu a Mali, sau biyu a Burkina Faso da kuma sau ɗaya a Jamhuriyar Nijar tun daga shekara ta 2020.
Sai dai sojojin da suka ƙarbe mulkin sun gaza cika alkawuransu na shafe ta’addanci tare da kawo karshen rikice-rikicen da suka haddasa asarar dubban rayuka baya ga miliyoyin da suka rasa muhallansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI