Akasarin masu aikin sa-kan sun tsere bisa tsoron kame ko kuma hare-hare, kana wuraren dafa abinci da su ka samar a ƙasar da aka yi kiyasin cewa ɗaruruwan mutane na mutuwa kullayaumin saboda cutukar da su ke da nasaba da yunwa sun daina raba abinci.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gana da 24 daga cikin masu aikin sa-kai da ke tafiyar da cibiyoyin dafa abinci a birnin Khartoum, yammacin yankin Darfur da wasu sassan yankin gabashin ƙasar, inda miliyoyin mutane su ka mtsere daga muhallansu tun da aka fara gwabza yaki tsakanin rundunar sojin ƙasar da daakarun RSF.
Wasu daga cikin masu aikin sa-kan da aka tattauna da su sun ce hukumomin agaji na ƙasa-da-ƙasa sun sun taima ka wa ƙungiyoyin da ke aikin sa-kai, amma hakan ya sa su yi ta kai musu hare-hare da zummar sata kayan abincin da aka ba su a matsayin gudummawa.
Wani ɗan aikin sa-kai da tuni ya arce daga birnin Khartoum, Gihad Salaheldin ya ce a lokacin mayaƙan RSF ba su da masaniya a game da gudummawar da ak ba su, sun zauna lafiya.
Dukkannin ɓangarorin da ke rikici da juna sun kai wa masu aikin sa-kan hare-hare bisa zargin su da hadin kai da abokan gabansu, kamar yadda gwamman masun aikin sa-kan su ka bayyana.
Akasarin masu aikin sa-kan sun buƙaci a sakaya sunayensu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI