Matashin da aka kama da zargin batanci ga gwamnatin Kamaru ya yi batan dabo- HRW

Matashin da aka kama da zargin batanci ga gwamnatin Kamaru ya yi batan dabo- HRW

Ƙungiyar ta yi zargin cewa an mayar da shi ƙasar sa a asali wato Kamaru bayan kamashi a Gabon.

An yiwa Akam mazaumin ƙasar Gabon sama da shekaru 10 ganin ƙarshe a wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, lokacin da jami’an tsaro suka sanya masa ankwa tare da tafiya da shi.

Fitaccen ɗan gwagwarmayar da aka fi sani da suna Ramon Cotta a shafinsa na Tiktok da ke da mabiya sama da dubu 30, yayi kaurin suna wajen chachakar gwamnatin Paul Biya da muƙarraban sa, musamman a yankin masu amfani da turancin ingilishi na ƙasar.

Ƙungiyar ta Human Righst Watch ta yi Allah wadai da kamun matashin, tana mai kwatanta hakan da ƙoƙarin hana jama’a faɗar albarkacin bakin su da kuma yi musu barzana da gwamnatin Kamaru ke yi.

Har yanzu dai gwamnatin Kamaru, ko kuma jami’an tsaro basu ce komai game da kamun nasa ba, kuma har yanzu tawagar lauyoyin matshin basu da wani cikakken bayani game a inda  yake.

Tuni dai jagoran adawar ƙasar Maurice Kamto ya buƙaci gwamnati ta yi gaggawar bayyana inda matashin yake.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)