Matar madugun 'yan adawar Uganda ta yi zargin take hakkin mijinta

Matar madugun 'yan adawar Uganda ta yi zargin take hakkin mijinta

Winnie Byanyima ta ce a makon jiya ne, aka cafke mijin nata, lokacin da yake shirin halartar taron kaddamar da wani littafi a Nairobi, abin da hukumomin kare hakkin dan adam irin su Amnesty International da ma’aikatar harkokin wajen Kenya suka bayyana a matsayin garkuwa.

Wata kotun sojin kasar ce dai ke tuhumarsa da laifin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba hadi da wasu laifuka da ake zarginsa da aikatawa.

Kakakin gwamnatin Uganda, Chris Baryomunsi y ace babu wani abu mai kama da garkuwa da aka yi da shi, illa iyaka dai aikin hadin gwiwa da aka yi tsakanin hukumomin tsaron kasashen biyu.

Byanyima ta ce tuhumar da ake yiwa mijinta nata wata bita da kullin siyasa ce, abin da kakain rundunar sojin kasar, Felix Kulayigye y ace kotu za ta yi amfani da dokokin da suka dace wajen aiwatar da bincike a kansa.

Besigye ya kasance na hannun dama kuma likitan Museveni.

‘yan adawar Uganda da masu fafutukar kare hakkin dana dam, sun jima suna zargin gwamnatin Museveni da amfani da kotun soji wajen hukunta masu adawa da gwamnati, zargin da gwamnatin ta musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)