A yanzu haka dai a ƙasar Kenya mata sun fara neman samun horo kan yadda zasu riƙa baiwa knasu kariya daga muzgunawar da suke fuskanta da har wasunsu ke rasa rayuwarsu.
Matan sun dauki wannan mataki ne sakamakon yadda ake yiwa ‘yan’uwansu mata kisan gilla da muzgunawa.
Inda abaya-bayannan aka samu gawar wata mace da aka kashe a wani gidan hawa kuma aka daddatsa ta sai wata ‘yar tseren gasar Olympics da wani saurayin ta ya ƙona, wannan ta’asa ta sanya mutane da dama a ƙasar ta Kenya ɗaukar matakan kare kai.
Akalla mata 97 ne aka kashe a fadin Kenya a kisan gilla da aka yi da gangan tare da wasu dalilai dake da alaka da matsalar jinsi, a tsakanin watan Agusta da Oktoba na shekarar da ta gabata, a cewar alkaluman ‘yan sandan ƙasar suka bayyana.
Masu fafutuka sun ce ana samun ci gaba a baya-bayan nan a duk fadin kasar Kenya da ke fama da talauci, inda kokarin da mata ke yi na kare kansu ya dauki sabon salo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI