Birnin mafi girma da mahimmanci a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya kasance fagenn daga tun bayan da mayaƙan ƴan tawayen M23 su ka kutsa ciki a daren Lahadin da ya gabata, bayan makwannin da su ka shafe su na ƙoƙarin yin hakan.
A Kinshasha, babban birnin ƙasar, masu zanga-zanga da su ka fito su na sukar rashin ɗaukar mataki a kan abin da ke faruwa a gabashin ƙasar daga manyan ƙasashen duniya ssun kai hari kan ofisoshin jakadancin Faransa, Belgium, Amurka da Rwanda da na wasu ƙasashen Afrika.
Babban sakatare a ma’aikatar harkokin wajen Kenya, 's Korir Sing'Oei, wani sako da ya wallafaa shafnsa na X, ya caccaki hare-haren da masu zan-zangar da ke bayyana rashin jin daɗin su su ka kai ofisoshin jakadancin Kenya, Uganda da Afrika ta Kudu.
Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot ya soki harin, inda ya ce yanzu an kashe wutar da aka banka wa ofishin jakadancin na Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI