Masu yunƙurin juyin mulki na gab da fuskantar hukuncin kisa a Congo

Masu yunƙurin juyin mulki na gab da fuskantar hukuncin kisa a Congo

Mai shigar da ƙara da ke wakiltar ɓangaren gwamnati a wannan shari’a Laftanal Kanar Innocent Rabjabu, ya bukaci alkalai su yanke hukuncin kisa akan mutanen su 50 saboda  samunsu da laifin zagon ƙasa, ta’addanci, yunƙurin kisa da kuma haɗa baki domin aikata kisa.

Abin tuni a nan shi ne, da asubahin ranar 19 ga watan mayun da ya gabata, wasu mutane ɗauke da makamai sun kai farmaki a  gidan tsohon ministan tattalin arziki, wanda a yanzu ke riƙe da shugabancin Majalisar Dokokin  kasar Vital Kamerhe, kafin daga bisani su afka wa ginin da ke ɗauke da ofishin shugaban ƙasar Felix Tshisekedi a birnin Kinshasa.

An dai yi nasarar murƙushe maharan, inda aka kaddamar da bincike tare da kama mutane 51 da ake zargin cewa suna da hannu a lamarin, yayin da aka fara yi musu shari’a a cikin wani gidan yari da ke birnin Kinshasa a ranar 7 ga watan yunin da ya gabata.

Uku daga cikin mutanen da ake tuhuma Amurkawa ne, sai ɗan Belgium daya, ɗan Birtaniya daya da kuma ɗan Canada daya, waɗanda aka bayyana cewa tuni suka samu takardun shaidar zama ‘yan asalin ƙasar ta Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)