Masu shiga tsakani sun ce an samu ci gaba a tattaunawar da ake yi kan yakin Sudan

Masu shiga tsakani sun ce an samu ci gaba a tattaunawar da ake yi kan yakin Sudan

 

Masu shiga tsakani a tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Sudan sun bayyana nasarar samun amincewar ɓangarorin biyu game da shigar da kayakin agaji, a wani yanayi da tsananin buƙatar tallafi ke yawaita a ƙasar.

Tattaunawar wadda za a shafe kwanaki 10 ana yi a Switzerland na da wakilcin ƙasashen Saudiya da Masar da Haɗaɗɗiyar daular larabawa waɗanda ke fatan samar da daidaito a ƙasar, ko da ya ke ɓangaren sojojin da ke mulki sun ƙauracewa zaman.

Tuni dai kayakin agaji suka fara shiga ƙasar musamman ta iyakarta da Chadi a yammacin Juma’a.

Masu shiga tsakani karkashin jagorancin Amurka a ranar Juma'ar sun ce, sun samu sahalewar bangarorin da ke rikici da juna a Sudan a tattaunawar da ake yi a birnin Geneva na inganta hanyoyin samar da agajin jin kai, amma rashin zuwan sojojin Sudan cikin shirin ya kawo cikas ga ci gaban da aka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)